page 20.indd

Download Report

Transcript page 20.indd

20
Z
inariya
AMINIYA
Juma’a 21 ga Nuwamba, 2014
Sanyin idon kowace mace
DANDALIN NISHADI
Tare da
Bashir Musa Liman [email protected] 07036925654
Ban tava da-na-sanin shiga
harkar fim ba-Rukayya Tijjani
Hisba ta cafke finafinan batsa a Kano
Ruqayya Tijjani Ayagi ba ta daxe a harkar fim ba, amma ta fito a
manyan fina-finai, inda a yanzu tana xaya daga cikin jarumai
mata da ake damawa da su a harkar. Ta yi bayani yadda ta
fara harkar fim, matsalolin da ta fuskanta da nasarorin da ta
cimma da kuma burinta nan gaba a harkar. Ga yadda hirar
ta kasance:
ukumar Hisba ta
Jihar Kano ta kama
wasu fina-finan
batsa da aka fi sani
da (blue film) wanda aka shigo
da su jihar ta varauniyar hanya.
Rahotanni sun bayyana
cewa wasu mutane waxanda
ba a san ko su waye ba suka yi
jigilarsu daga Jihar Legas don
yin kasuwancinsu a Jihar Kano.
Ustaz Aminu Ibrahim
Daurawa shi ne Kwamanda
Janar na Hukumar Hisba
ya shaida wa Aminiya cewa
hukumarsu ta yi nasarar kame
waxannan fina-finan ne da
taimakon wani fasinja wanda ke
bin hanyar Legas.
“Wani fasinja ne ya sanar da
mu cewa akwai fina-finan batsa
da aka yi simogal xinsu a cikin
wata mota da ke kan hanyar
zuwa Kano. Ba mu yi qasa a
gwiwa ba muka tura jami’anmu
inda suka gano mana wasu
jakunkuna waxanda suke cike
maqil da fina-finan batsa, inda
yawansu ya fi 700.” Inji shi.
Kwamandan ya qara da cewa
“Baya ga fina-finan batsa da ke
cikin jakunkunan, hukumarmu
ta cafkemagungunanqaraqarfin
maza da ke cikin jakunkunan,
wato ire-iren magungunan
da likitoci ke bayarwa ga irin
mutanen da ke da rashin lafiyar
gaba. Wannan yana nuna cewa
masu waxannan kaya suna
nufin su lalata mana tarbiyyar
yara”. Inji shi.
Da yake jawabi game da
irin matakin da hukumar Hisba
ke shirin xauka a kan lamarin,
Daurawa ya bayyana cewa zuwa
yanzu ba su gano waxanda ke
da alhakin shigo da fina-finan
ba. “Zuwa yanzu ba mu gano
masu fina-finan ba, amma duk
lokacin da muka same su za mu
yanke musu hukunci daidai
da laifinsu. Ba za mu yarda mu
zuba ido saboda abin duniyar da
wasu tsiraru za su samu ta hanyar
sayar da wannan fina-finai, mu
kuma tarbiyyar ’ya’yanmu ta
lalace ba. Kasancewar babu abin
da ire-iren waxannan fina-finai
ke koyarwa sai vata tarbiyya,
domin a nan ne ake koyon
zina da luwaxi da maxigo da
sauransu. Haka kuma daga
kallon waxannan fina-finai ake
qara samun yawaitar laifukan
fyaxe a cikin al’umma. A shirye
muke mu xauki tsattsauran
mataki a kan irin waxannna
mutane” Inji shi.
Ya yi kira ga al’ummar
Musulmi da su zama masu kula
da tarbiyyar ’ya’yansu ta hanyar
sa ido a kan irin fina-finan da
suke kallo, kasancewar matasa
ne suka fi kallon irin waxannan
fina-finai.
Daga Ibrahim Giginyu
da Bashir Musa Liman
Za mu fara da tarihinki
a taqaice?
unana
Ruqayya
Tijjani Ayagi, an
haife ni a Kano.
Na yi makarantar
firamare da sakandare a
Kano. Daga nan ban ci
gaba da karatu ba, amma
dai na ci gaba da zuwa
makarantar Islamiyya.
Me ya ja hankalinki
kika fara harkar fim?
Tun ina qarama nake
kallon fina-finan Hausa,
hakan ya sanya na fara
sha’awar in kasance xaya
daga cikin masu shirya
fina-finan Hausa, wato a
matsayin jaruma ko dai
xaya daga cikin masu
ruwa da tsaki a harkar.
Nakan faxa wa mahaifiyata
burina in zama jaruma, a
lokacin ba ta cewa komai
face ta yi dariya, domin ta
xauka yarinta ce, amma
har cikin zuciyata burina
ke nan, abin da ban
tambayi kaina ba shi ne,
wace hanya ko mataki zan
bi don shiga Kannywood.
Na dai ci gaba da faxa wa
mahaifiyata, amma ba ta
tava dakatar da ni ba, abin
da take cewa shi ne, “yata
a kowace sana’a a rayuwa
akwai mutanen kirki da
S
kuma vata-gari, amma ina
da yaqinin ba za ki tava
zama daga cikin vata-gari
ba, idan har harkar fim kike
so ki yi, to ina miki addu’ar
samun nasara.” A lokacin
ma ban yanke shawarar
fara harkar fim ba har na
yi aure, kodayake aurena
ya mutu tun ba a je ko’ina
ba. Na yi dukkan haqurin
da zan yi don ganin aurena
bai mutu ba, amma abin ya
ci tura, jim kaxan bayan
na haifi ’yata ne auren ya
mutu. Daga nan ne na roqi
iyayena su amince in shiga
harkar fim. Bayan sun
amince ne sai shiga harkar
gadan-gadan.
Waxanne matsaloli
kika fuskanta?
Zan iya cewa ban
fuskanci matsaloli masu
yawa ba, kasancewar tun a
farko iyayena sun amince
mini. Ba wani abin voyevoye ba ne cewa yawanci
mutane suna ganin ’yan
fim a matsayin vata-gari,
inda suke sukar su ba tare
da qwararan hujjoji ba,
hakan ya sanya ’yan uwa
da abokan arziki suka qi
amincewa in shiga harkar
fim, amma sakamakon
yadda na kare mutuncina
sai suka fahimci ina cikin
sana’a mai kyawu ce,
sannan suka riqa yi mini
addu’ar samun nasara a
harkar.
Jaruma Ruqayya Tijjani (a dama) da Jamila Nagudu
A kullum ina cikin farin
ciki sakamakon sa’ar iyaye
da na yi masu fahimta,
sun ce mutum zai kasance
na banza ne idan ya zavi
kasancewa hakan. Abin da
ya ba mutane mamaki shi
ne, ban sha wahala wajen
zama jaruma ba, kamar
yadda sauran jarumai
masu tasowa suka fuskanci
qalubale sosai, sannan
manyan harkar sun karve
ni hannu bibbiyu.
Yaya kika ji a ranar
farko da aka xora miki
kyamara?
Na ji wani iri, sai
na ji kamar ina cikin
mawuyacin hali, na faxa
wa kaina wannan ne
lokacin da zai tabbatar da
ko dai in burge furodusa
da darakta ko kuma akasin
haka. Na yi sa’a daraktan
ya riqa cewa in kwantar
da hankalina. Daga baya
jama’a suka riqa faxa mini
na yi qoqari, domin ba su
tava tsammanin sabuwar
jaruma za ta qoqarin da na
yi ba, inda na ci gaba wanda
a yanzu ban san yawan
fina-finan da na yi ba.
Waxanne fina-finai
kika yi?
Kamar yadda na faxa
tun a farko, ina kallon
kaina a matsayin jarumar
da ta taki sa’a, domin cikin
xan qanqanen lokacin da
na yi a harkar fim na yi
fina-finai masu yawa da
ya fi na sauran jaruman da
na tarar a harkar. A yanzu
da nake magana ba zan iya
qirga yawan fina-finan da
na yi ba. Fina-finan da na
yi sun haxa da ‘Hanyar
Abuja’ da ‘Ranar Suna’ da
‘Gidan Haya’ da ‘Auren
Soja’ da sauransu. Ni ce
babbar jaruma a fim xin
’Yan Bodin.
Me yake sa ki farin ciki
idan aka ambaci harkar
fim?
An ba ni kyaututtuka
masu yawa, waxansu ma
daga wurin mutanen da
ban san su ba, ban tava
ganin su ba. Sukan faxa
mini cewa sun ga finafinaina ne, rawar da na taka
ta burge su. Duk ranar da
aka ba ni kyauta, ko aka
yaba mini sakamakon rol
xin da na taka a wani fim
sai in ji farin ciki ya lulluve
ni.
Ko kin tava da-na-sanin
shigar harkar fim?
Ban tava da-na-sanin
shiga harkar fim ba, ina so
sana’ar sosai.
Wane buri kike da shi a
harkar fim?
Burina in kasance
xaya daga cikin manyan
jarumai, wanda tarihi ba
zai tava mantawa da su ba.
Ina so in yi wani abu da zai
gyara rayuwar jama’a ta
hanyar fina-finan da zan
riqa yi, wanda hakan zai
sa a riqa tunawa da ni. Ina
so ’yan baya su riqa koyi da
ni, sannan su riqa alfahari
da ni.
Yaya batun aure kuma?
A yanzu dai babu
batun aure saboda ba ni da
manemi. Ina tare da wani
amma a yanzu mun samu
savani.
Mutuwar Darakta Saleh AGM ta jijjiga Kannywood
Daga Bashir Musa Liman
M
uturwar
fitaccen
darakta Saleh AGM
ta jijjiga masana’antar
fina-finan Hausa.
Marigayin ya mutu ne a ranar
Asabar sakamakon haxarin mota
a lokacin da yake kan hanyarsa ta
koma wa Maiduguri daga Abuja,
bayan ya kammala xaukar fim xinsa
mai suna ‘Mallaka Min Dukiyarki’
Wata majiya ta ce motar marigayin
ta faxa cikin wani rami ne a lokacin
da yake tuqi, hakan ya sanya ta riqa
wuntsulawa a qarshe ya rasu bayan ya
ji munanan raunuka da suka haifar
da zubar jini sosai.
Fim xin wanda ya haxa da jarumai
kamar su Yakubu Muhammad da Ali
Nuhu da Rahama Sadau da Tijjani
Faraga da Rabi’u Rikadawa da Sadiq
Sani Sadiq da sauransu, marigayin ne
ya rubuta shi, ya kuma ba da umarni.
George Onmonya Daniel abokin
marigayin ya ce mutuwar ta jijjiga
shi.
“Duk lokacin da Saleh AGM ya
zo Abuja to a gidana yake sauka,
ko a kwanakin baya da ya zo Abuja
yana neman wuraren da zai xauki
fim xinsa mai suna ‘Mallaki Min
Dukiyarki’ a gidana ya zauna. Na
je wurin da ake xaukar fim xin, har
na tattauna da Ali Nuhu da Yakubu
Muhammad. Jiya (Juma’a) da misalin
11:29 na dare muka yi magana da
shi ta waya, a lokacin barci ya fara
kama ni, ashe sallama na yi da shi.
Mutuwarsa ta jijjiga ni, Allah Ya ji
qansa.”
Rahama Sadau ta ce sai ta ji kamar
mafarki take yi da aka faxa mata
mutuwar daraktan.
“Ina xaya daga cikin jaruman da
ke fim xin ‘Mallaka Min Dukiyarki’,
ana cikin xaukar fim xin mun yi wasa
da dariya sosai, lokaci zuwa lokaci
yakan zolaye ni, na karanta labarin
mutuwarsa a shafin twitter ne, na
kaxu sosai. Na ji kamar a mafarki,
sai na ce ko dai wasa ne kamar yadda
aka saba yi wa ’yan fim, amma daga
baya na bincika sai na tabbatar da
mutuwar.” Inji ta.
Yakubu Muhammad ya ce za a
daxe kafin a cike givin da marigayin
ya bari ba, domin ya san aiki, kuma
yana gudanar da harkokinsa bisa
tsari.
Marigayi Saleh AGM
Daga Lubabatu I. Garba,
Kano
H