Transcript aminiya
5 AMINIYA Juma’a, 10 ga Oktoba, 2014 WASIQU Saqonnin waya Buhariyya-Aqida Muna miqa saqon bangajiya ga ximbin jama‘ar da suka halarci taron qungiyar magoya bayan Janar Muhammadu Buhari mai suna ‘ Buhariyya-Aqida‘. Wadda aka gudanar a wannan Litinin da ta gabata, a garin Hadejia da ke Jihar jigawa. Da fatan kowa ya isa gidansa lafiya. Allah ya taimaki janar Baba Buhari, ya ba shi mulkin Nijeriya. Daga: Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382. Ga shugabannin Arewa Salam Edita barka da aiki ina so ka ba ni dama inyi kira ga shugabanin Arewa cewa ya kamata su tashi tsaye gurin ceto al’ummar yankin daga wanan hali da muke ciki a yan zu na rashin tsaro da ci gaba na yau da kullum da fatan za su tausaya mana don ci gaban yankin namu dama qasar baki xaya. Daga Umar Idirisa Bapps Askira jihar Borno 07034478412. Martani ga Muktar Shagari Maganar da ya yi na cewa, shugaba Goodluck ya yi ayukan alheri a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce, “Goodluck ya yi aikin Titi a Gusau zuwa Kontagora,” wannan magana zuqitamalle ce, don gaskiya kowa ya san cewa titin Sakwato da na Shagari da na Tambuwal da na Aleiro da na Jega da na Koko da na Yawuri da na Kontagora duk sun zama tarkon Mutuwa. Don haka Muktari Shagari da ma munsan dacewa ‘ba’a mugun sarki, sai mugun Bafade. Komai nisan jifa qasa za. Allah ya raka taki gona. Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. Gsm 07037697009. Addu’ar tsari daga zalunci Edita ka ba ni dama don in isar da addu’ar neman tsari ga al’ummar Najeriya. Don haka ma nike ganinmu karanta Suratul Munafiqun qafa 10, don Allah ya kawo mana qarshen zalunci da makircin munafukan qasar nan. Daga A.A. U 08151767785. A kula da direbobi Aminiya don Allah ina da fatawa, Wai me yasa gwamnati ba ta kulawa da direbobi ne? Misali hanyarmu ta Kaduna zuwa Legas ba kula da ita, kuma me yasa haka? Daga Ibrahim 08054517672. Ga Sarkin Kano Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka ba ni dama in miqa saqon taya murnar Babbar sallah gaMaimartaba Sarkin Kano. Da fatan ya yi sallah lafiya, tare da iyalansa. Allah Ya qara wa Sarki lafiya da nisan kwana. Amin. Daga Yunusa Hamza 08133183507. Ga’yan takarar APC Edita kabana dama in roqi ya takarar shugabancin qasar nan a APC ,waxanda suka haxa da Kwankwaso da Atiku da su haqura su bar wa Buhari takara. Domin mu dai a faxin Arewacin Najeriya ba mu da kamar Janar Muhammadu Buhari Mai gaskiya. Muna kuma roqon Gwamna Kwankwaso da ya tsayar mana da Janar Jafaru Isa amatsayin xan takarar Gwamnan, domin shi ma yana da nagartar da ta fita sauran ’yan takara a jihar Kano. Muna fatan Allah Ya yi mana zavi mai amfani. Ya kuma ba mu basira kada mu yi zaven tumun dare. Daga Ahmad Tiga 08068643445. Ga Aminiya Salamu alaikum. Aminiya da fatan kun yi sallah lafiya. Allah Ya maimaita mana. Kuma ya jimamin makaman da ake shigowa da su don wargaza Najeriya. To, Allah Ya tsare mu daga sharrin masu makirci. Amin. Daga 08126466663. Ga jama’ar Arewa Salam. Jama’ar Arewa Musulmi da Kirista mu haxa kai,mu manta da bambanicin qabila da na addini. Don mu gudu tare, mu tsiratare. Kwankwaso ka sanya mu tagumi ditan Aminiya, wadda ta samu karvuwa a wannan qasarbaki xaya, ka ba ni dama in bayyana takaicina kan yadda Gwamna Kwankwaso ya sanya mu tagumi, a tsawon mulkinsa, tun daga 1999 zuwa 2003, dakuma dawowarsa a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2014. Haqiqa rusau xin da aka yi a titin Ibrahim Taiwo, an cutar da mu, E domin gidajen tun a shekarar 1934, Gwamnatin Arewa ta bai wa Alhaji Alhassan Xantata, kuma mahaifinmu ya sayi wasu a hannun xan uwansa, Alhaji Sanusi Xantata, cikin shekarar 1964. Sannan ’yan KAROTA ma ba mu daxinsu ba, domin kai da kanka ka bayyana cewa ba masu ilimi ka sanya ba. Sannan Mai girma Gwamna muna zargin ka rushe masallatai a qalla 401. Akwai al’amura da dama waxanda idan muka bayyana su sai a ce adawa ce kawai, amma haqiqanin gaskiyarmu muke bayani a kai. Don haka akwai buqatar ka wanke kanka kafin wa’adin mulkinka ya qare, ko kuma, waxanda aka zalunta su ci gaba neman haqqinsu wajen Allah. Daga Sabo Muhammad Ilori, Gida Mai Lamba 64, Unguwar Gabari. Allah Ya qara tona asirin masu shirin wargaza mu. Amin. Daga 08059044449. yi hawan sallah, amma waccan sallar da tagabata,wato aramar sallah, ba ku yi hawa ba. Kun ce saboda matsalar tsaro. To yanzu tsaron ya ingant ane. Ku faxi gaskiyar abin da ya hana ku hawa. Daga 08117896000. Ina son ka yi mana cigiyar abokina Ibrahim Custom, wanda ke zaune a Sabon gari Zariya. Domin kwana biyu bamu ji xuriyarsa a Aminiya ba. Ko ya daina rubutu ne? Daga 08167569141. Ga Janar Buhari Aminioya ’yar aman don Allah ku miqa min saqon “Barka da Sallah” ga jagoran APC na qasa, Shugaban asa na 2015, Janar Muhammadu Buhari, tare da al’ummar Musulmin duniya baki xaya. Da fatan an yi sallah lafiya. Daga Musa Unguwar Mai Yasin, Xanja, Jihar Katsina 08155648155. Barkada sallah Edi Mubarakun ga xaukacin Musulmin duniya.Kuma muna addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Nagode Edita. Daga 07060799679. Mu dage da addu’a Ya ku ’yan uwana talakawa,ba zargin shugabanni ne mafita ba. Hakan ma qara kawo mana bala’I yake yi.. Mu dage da addu’a. Daga 08079156747. Ga xan sanda mai lambar yabo Editan Aminiya ina taya xan sanda kula da ababen hawa”Traffic Police,”da shugaban qasa ya karrama da lambar yabo. Daga 08034275846. Ga Sarakunan gargajiya Sarakunan gargajiya, na ga kun Ina Ibrahim Kwastom? Edita Allah Ya kare mana kai. Ga Gwamna Wamako Edita ka bani dama in miqa saqona ga Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako, Sarkin Yamma kan alqawarin da ya yi mana na hanya da gada a Dukamaje. Daga Alhaji Sani Abubakar Dogon Daji 08032238844. Ga Takai xan takarar Gwmnan Kano Fatan alheri ga xan takarar Gwamnan Kano a qarqashin tutar jam’iyyar PDP, Malam Salihu Sagir Takai. Da fatan ya yi sallah lafiya. Allah Ya yi jagora. Daga 08166835313. AMINIYA KABIRU A. YUSUF Shugaba kuma Babban Jamiín Gudanarwa ISIAQ AJIBOLA Manajin Darakta kuma Babban Jamiín Aiwatarwa MANNIR XAN ALI Daraktan Gudanarwa kuma Babban Edita MAHMUD JEGA Mataimakin Darakta (Vangaren Labarai) ALIYU M. AKOSHILE Mataimakin Darakta (Harkokin Kasuwanci) BALARABE LADAN Muqaddashin Edita SHEHU O. MOHAMMAD Janar Manaja, Harkokin Gudanarwa GARBA ALIYU ABUBAKAR Na’ibin Janar Manaja Harkokin Sadarwa AKEEM MUSTAPHA Manajan Tallace-Tallace i-mail: [email protected]; Intanet: www.aminiya.com.ng Tes: 08075129644