bakake da wasulan hausa class: ss3 teacher: mrs

Download Report

Transcript bakake da wasulan hausa class: ss3 teacher: mrs

DOWEN COLLEGE LAGOS DEPARTMENT OF LANGUAGES SUBJECT: BAKAKE DA WASULAN HAUSA CLASS: SS3 TEACHER: MRS OGUNDAMOWO E-MAIL ADDRESS: [email protected] Batu:- Yanayin Furci

Yanayin furci yana nufin irin tangardar da iska ke samu ne a yayin furcin baki. A yayin furta baki iska takan sami tangarda ko cikas kafin ta samawa kanta hanya fita. Dalili shi ne haduwar gabobin sauti da junan su, ko kusanta juna. Wato duk lokacin da su ka hade, za su datse iskar ta rasa mafita har sai sun saki juna. Misali a wajen furta /b/, in lebe ke datse wannan iskar. Haka ma lokacin da gababi suka kusanci juna iska kan sami tangarda domin hanyar da za ta bi ya ragu ainun.

Muhallan Furci

Wannan shi ne gurabe daban-daban na cikin baki in da sauti ke fita

Rukunnin /b/,/m/

A wajen furta wadannan Bakake dole ne leben kasa da na sama su hade waje guda. Don haka tun da muhallin furcin dukkansu ya shafi lebe ne ana ce da su

lebawa.

Kowane daya ana ce da shi

balebe

Rukunnin /t/, /d/, /s/, /z/, /n

/.Furcin wadannan tsinin harshe ne da hanka ke yin aikin gaba daya. A wajen furcin /s/,da /z/gababen ba su haduwa sai dai sukan kusanci juna. Amma a furcin /t/, /d/, da /n/ tsinin harshe hadewa ya ke da hankar. Amma da shi ke ya shafi tsinin harshe da hanka ana kiran su

hankawa

. Kowannensu kuma an ace da shi

bahanke

Rukunnin /y/

A yayin furta wannan , gaban harshe zai daga ya doshi ganda .gabobin ba su haduwa, kuma ba su kusa da juna ba .Tazarar da ke tsakanin su tana da yar yalwa. Tunda furci ya shafi ganda da gaban harshe ana kiran sa

bagande

Rukunin /kw/,/kw/,/ky

/ Wannan ya bamban ta da sauran da muka koya. /Kw/, /kw/, da/gw/su ne yan goyo., a wajen furta su doron harshe da handa za su hade kamar wajen furta /k/,/k/, da /g/ sai a kewaye da lebe .kewaye lebba shi ne goyon da ake yi wa /k/,/k/,/g/ a sami /kw/, /kw/da /gw/. Furcin wadannan ya shafi doron harshe da handa tare da kewaye lebba an ace da shi

lebantattun handawa

. AIKIN GIDA LITTAFI

i.Darussan Hausa (na 3).shafi na 6-9 ii. Exam focus Hausa Language. Shafi na 65-66 a.

b.

A yi akin na 1.9 Darussan Hausa, lamba 1-3 A yi akin na 10.7.2 Exam Focus , lamba 1 da 5 Send your answers to the above e-mail address